Shugaban 'yan adawar Libya ya kai ziyara China

Mahmud Jibril Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahmud Jibril

Daya daga cikin manyan shugabannin 'yan adawan Libiya, Mahmoud Jibril, ya isa birnin Beijing domin yin tattaunawa da jami'an China.

Ziyarar ta biyo bayan ganawar da aka tabbatar an yi a watan da ya wuce a Qatar, tsakanin wani jami'in diplomasiyyar kasar ta Sin, da kuma shugaban majalisar wucin-gadi ta Libiyar, Mustapha Abdel Jalil.

A farkon wannan watan, ministan harkokin wajen Kanar Gaddafi ya ziyarci birnin Beijing.