Taron majalisar tsaron kasa a Najeriya

katsina
Image caption Ofishin 'yan sanda da bom ya daidaita a jihar Katsina

Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya shugabanci taron majalisar tsaro ta kasar, inda suka tattauna a kan tabarbarewar da al'amuran tsaro ke ci gaba da yi a kasar.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ake fama da hare-hare da kuma tashin bama-bamai a wasu yankunan Arewacin kasar.

Kasa da mako guda kenan da kungiyar Boko Haram ta kai hari a hedkwatar 'yan sandan Najeriyar da ke Abuja, inda mutane takwas suka hallaka.

Ko a ranar Litinin ma, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a caji ofis da kuma wani banki a garin Kankara na jahar Katsina, inda suka kashe kimanin mutane bakwai.

Wakilin BBC Ibrahim Isa, ya ce dukkan manyan jami'an tsaron kasar sun halarci taron wanda shugaba Jonathan ya jagoranta.

Sai dai ya ce ba su ce uffan ga 'yan jarida ba bayan kammala taron.

Suma 'yan sanda na su...

To bayan taron da shugaban na Najeriya ya jagoranta a kan batun tabbatar da tsaro a kasar.

Su ma shugabannin rundunonin 'yan sandan Najeriyar sun shiga ganawa --- duk dai a kan yadda za a shawo kan munanan hare-haren da ake ta kaiwa a baya-bayan nan a kasar.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron ya zo ne kwanaki kadan bayan harin da aka kai a hedkwatar 'yan sandan

Wakilin BBC Muhammad Abba wanda ya je hedkwatar rundunar 'yan sandan a Abuja, ya ce manyan jami'an 'yan sanda daga mukamin kwamishina zuwa sama ne ke halartar taron.

Duk da cewa ba su fito fili sun bayyana abin da za su tattauna ba, rahotanni sun ce za su maida hankali ne kan batun tabarbarewar tsaro a kasar.

Jonathan ya yi alkawari

Babban abin da 'yan kasar za su so gani a yanzu dai shi ne cika alkawarin da shugaba Jonathan ya yi na cewa za su kawo karshen wadannan hare-haren da ake kaiwa.

A lokacin da ya ziyarci hedkwatar 'yan sandan kasar, shugaba Jonathan ya ce jami'an tsaro na yin duk mai yi wuwa wajen kawo karshen hare-haren bama-baman.

Kuma wasu masu lura da al'amura na ganin mai yi wuwa tarurrukan na da nasaba da yadda gwamnatin kasar ke shirin tunkarar matsalar.

Ana dai dora alhakin yawancin hare-haren da ake kaiwa kan kungiyar nan ta Boko Haram, wacce ke fafutukar kafa tsarin shari'ar Musulunci a Arewacin Najeriya.