Za a kammala taron kwamishinonin 'yansandan Najeriya

Nigeria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana yawan kaiwa 'yan sandan hare-hare a 'yan kwanakin nan

A Najeriya, a yau ne kwamishinonin 'yan sanda na jihohi 36 dake kasar ke kammala wani taro da suka fara a jiya game da tabarbarewar harkar tsaro a kasar.

Taron dai shine irinsa na farko da shugabannin 'yan sandan suka gudanar, tun bayan harin bama-baman da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram, suka yi ikirarin cewa sune suka kai a hedkwatar 'yan sandan da ke Abuja, inda mutane takwas suka hallaka.

Hare-haren bama-bamai dai na ci gaba da karuwa a wasu sassan Najeriyar, abinda masu sharhi ke ganin cewa ya zama wani babban kalubale ga jami'an tsaro a kasar.

Alhaji Ibrahim Babankowa wanda tsohon kwamishinan 'yan sanda ne, kuma masani ne akan harkokin tsaron cikin gida a Najeriyar, ya shaidawa BBC cewa akwai bukatar ganin cewa an maida hankali wurin tabbatar da tsaro a caj ofis din 'yansanda.

Ya kuma ce akwai bukatar ganin an yi amfani da tsoffafin shugabannin jami'an tsaro akan yadda za'a shawo kan matsalar.