An kashe mutane bakwai a wani artabun da aka yi a Syria

Rahotanni daga Syria sun ce an kashe akalla masu zanga zanga bakwai a arangamar da aka yi tsakanin masu goyan bayan gwamnati da masu kin jininta a garuruwan Homs da Deir al-Zor.

Masu fafutuka sun ce jami'an tsaron Syria sun goyi bayan wadanda ke bayan gwamnati, inda rahotanni suka ce wani yaro dan shekara goma sha hudu na daga cikin wadanda aka kashen.

Tun da farko gidan talabijin din kasar ta Syria ya nuna hotunan bidiyon wasu mutane dake gangamin goyan bayan shugaba Bashar al-Assad a garuruwa da birane da dama na kasar.