'Yan sandan China sun saki Ai Weiwei

Ai Weiwei Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An bada belin Ai Weiwei

An bada belin daya daga cikin masu fasahar zane zanen kasar China mafi shahara, wato Ai Weiwei.

Ai Weiwei ya share fiye da watanni biyu a tsare a wurin 'yan sanda.

An dai ruwaito shi yana cewa, ya amsa laifin kin biyan haraji amma kuma yayi alkawarin biya.

Ai Weiwei ya shaidawa BBC cewa, yana gida zaune, a matsayin beli, kuma lafiyarsa kalau, amma ba zai yi magana da manema labarai ba.

A watan Afrilu ne aka kama Ai Weiwei, mai fitowa fili yana sukar gwamnatin China ta kwaminisanci.