Amurka za ta janye sojojinta daga Afghanistan

Shugaba Obama
Image caption Amurka za ta janye dakarunta daga Afghanistan

Shugaban Amurka Barack Obama ya ba da sanarwar janye dakarun Amurka fiye da dubu talatin daga Afghanistan nan da watan Satumban badi.

Da ya ke jawabi a fadar gwamnatin Amurka ta White House, Shugaba Obama ya ce Amurka za ta fara ne da janye dakaru dubu goma daga kasar ta Afghanistan.

Ya ce: ''Za mu kuma fara ne daga watan gobe. Kafin bazarar badi kuma, za mu kammala kwaso sojojinmu dubu talatin da uku''.

Shugaba Obama ya bayyana janyewar a matsayin matakin farko na kawo karshen yakin Afghanistan da kuma mayar da alhakin tsaro a hannun sojojin kasar ta Afghanistan.

Sai dai manyan jami'an rundunar sojin Amurka, basu ji dadin matakin janye sojojin ba, inda suka ce sun so ne a janye su da kadan-kadan.

Amma kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa, 'yan kasar sun ji dadin jawabin na Shugaba Obama.