Hukumomin Bahrain sun yi wa masu fafutika daurin rai da rai

Zanen zaman kotu a Bahrain Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Zanen zaman kotu a Bahrain

Wata kotun soji a Bahrain ta yankewa 'yan adawa takwas hukuncin daurin rai da rai, bayan da ta same su da laifin shirin kifar da gwamnati a lokacin da aka yi ta zanga zanga a kasar a farkon wannan shekarar.

An kuma yankewa wasu goma sha uku hukunci mai sassauci kama daga daurin shekaru biyu zuwa goma sha biyar a gidan kaso.

Bayan da aka karanto musu hukuncin, wadanda ake karar sun yi ta rera wakoki tare da jaddada yanayin zanga zangarsu ta lumana.

Wakilin BBC ya ce shugabannin Bahrain sun shirya wata tattaunawa ta kasa, amma abin tambayar a nan ita ce ko ya wannan hukuncin zai shafi tattaunawar.