BBC na juyayin kama wakilinta a Tajikistan

110622171228_urunboyusmonov_bbc_226x170_bbc_nocredit.jpg
Image caption Kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida sun yi Allah wadai da kamen na sa

'Yan jaridar BBC sun yi wata tsayuwa a birnin London domin juyayi da kuma neman a sako abokin aikinsu da aka kama a kasar Tajikistan.

Ana tsare Urunboy Usmonov ne tun kwanaki goma da suka wuce a hannun hukumomin tsaron kasar da ke garin Khojand a Arewacin Tajikistan.

Kuma a wannan makon ne aka tuhume shi da hada kai da wata kungiyar masu tsattsaurar ra'ayi.

Sai dai BBC ta ce zargin cewa Mr Usmonov mamba ne a kungiyar Musulunci ta Hizb ut-Tahrir wacce aka haramta ba shi da tushe.

Bayan tsare shi ba tare da an bar wani ya ganshi ba, iyalansa sun ce an basu damar ganinsa na sa'a guda da rabi.

BBC ta nemi a gaggauta sako shi

Matarsa Malohat Abduazimova, ta shaidawa BBC cewa hankalinta ya tashi lokacin da ta ga mijin na ta.

"Da kyar na gane shi", "Babu kwari a jikinsa kwata-kwata. Na fahimci cewa da kyar yake magana."

A lokacin da yake tsare, an bar wasu 'yan jarida biyu sun gana da shi, inda a rahotanninsu suka alakanta shi da kungiyar Hizb ut-Tahrir.

A wata sanarwa da BBC ta fitar, ta yi watsi da rahoton 'yan jaridar, tana mai cewa sun sabawa ka'idojin aikin jarida.

Kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida sun yi Allah wadai da kamen na sa, suna masu cewa yunkuri ne na dakile rahotanni kan al'amuran siyasa masu tsauri.

BBC na neman a gaggauta sako Mr Usmonov.