Gaddafi ya yi suka kan NATO

Mu'ammar Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gaddafi ya yi suka kan dakarun NATO

Shugaba Mu'ammar Gaddafi na Libya ya zargi kungiyar tsaro ta NATO da kashe fararen hula a hare-haren da ta ke kaiwa kan dakarunsa.

A wani sako da aka yada ta gidan talabijin na Libyan, Kanar Gaddafi ya ce karya NATO ta sharara da ta ce tana iya bakin kokarinta don kaucewa kai hari a kan farar hula.

Wannan shi ne martani na farko da ya mayar a kan hare-haren da NATO ta kai, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar dangin wani na hannun damansa.

Shugaba Gaddafi ya ce tura-ta-kai-bango dangane da hare-haren da ake kaiwa a kasar.

Ya ce zai ci gaba da kalubalantar kasashen Yamma, wadanda ya ce suna fada da addinin Musulunci, har sai ya ga bayansu.