Ana taron manyan jami'an yansanda a Abuja

Manyan Jami'an 'yansanda a Najeria na cigaba da taron da suka fara a jiya don bullowa tabarbarewar harkar tsaro a kasar.

A makon da ya gabata ne, 'yan Kungiyar nan ta Ahlus Sunna Lil-da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram ta kai harin bam a hedkwatar rundunar 'yan sanda ta kasa da ke Abuja, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da kuma dukiyoyi.

Ana yin wannan taro ne dai yayinda mutane da dama ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da hanyoyin da ya kamata a bi wajen kawo karshen hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar ta Jama'atu Ahlussuna Lidda'awati Wal jihad ne ke kai su.