Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kammala taronta

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kammala wani taro na kwanaki biyu, game da batun tabarbarewar tsaro a kasar, ba tare da ta yi bayyani akan abubuwan da ta cimmawa ba. An yi tsammanin a wajen taron za a tabo batun kungiyar nan ta Boko Haram, wadda ake zargi da kai hare hare da kuma dasa bama bamai.

To amma babu inda aka ambaci sunan kungiyar ta Boko Haram a wajen taron 'yan sandan.

A makon da ya gabata ne kungiyar ta Boko Haram, wadda kuma ake kira Ahlus Sunna Lil-da'awati wal Jihad, ta kai harin bam a hedkwatar rundunar 'yan sandan ta kasa dake Abuja.

An sami hasarar rayuka da dukiya a lokacin harin.