Kaddamar da riga-kafin cutar Polio a Nijar

Mahamadou Issoufou
Image caption Taro kan riga-kafin polio a Nijar

A jamhuriyar Nijar, a yau Alhamis ne hukumomin lafiya tare da tallafin wasu kungiyoyin da suka hada da asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya, za su kaddamar da aikin riga-kafin kamuwa da cutar Polio ko shan-inna a kan iyakokin kasar.

Ana sa ran yiwa yaran Nijar, wadanda ke jihohin da ke da iyaka da kasashe kamar Najeriya, da Benin da Chadi, allurar riga-kafi da zummar kare su daga kamuwa daga kwayoyin cutar.

Rahotanni sun ce yaro daya ne ya harbu da kwayoyin cutar Polio bana a kasar.

Taron dai zai hada manyan jami'an kula da kiyon lafiya.