Syria ta yi kakkausar suka a kan turai

Ministan kula da harkokin waje na kasar Syria, Waleed Mo'allem, ya zargi ministocin kasashen Turai da haddasa rikici tare da jawo rudani a kasar.

Minista Mo'allem ya shaida wa manema labarai cewa kasarsa za ta manta da kasancewar turai gaba daya a taswirar duniya,ta juya akalar huldar siyasa da tattalin arzukinta zuwa kudanci da kuma gabacin duniya.

Yace,"ba nahiyar turai kadai ba ce a duniya kuma Syria za ta yi tsayin daka kamar yadda ta yi tun shekara ta 2003, kamar yadda a wancan lokacin ta kubuta daga irin saniyar waren da akai mai da ita, a yanzu ma za ta iya shawo kan matsalar da take fuskanta".

Minista Mo'allem ya kwatanta takunkumin da Turai tasa wa Syria a matsayin wani yaki da kasar, wanda ya ce zai shafi rayuwar jama'a.