An rantsar da sabon Fira Ministan Somalia

Abdiweli Mohamed Ali Hakkin mallakar hoto o
Image caption Abdiweli Mohamed Ali ba bako ba ne a siyasar Somalia

Shugaban rikon kwarya na Somalia Sharif Sheik Ahmed, ya nada Abdiweli Mohamed Ali, a matsayin Fira Minista a wani biki a fadar shugaban kasa a birnin Mogadishu.

Babban kalubalen da ke gabansa shi ne na samun goyon bayan Majalisar Dokoki ba wai kawai kan nadin nasa ba, harma da majalisar ministocin da zai nada a 'yan makwanni masu zuwa.

Baya ga nan ne kuma zai fuskasnci matsalar tsaro da harkokin siyasa da na tattalin arziki. Shi dai ba bako bane a fagen siyasar Somalia.

Watanni goma sha biyu ne dai suka ragewa gwamnatin rikon ta Somalia domin gudanar da ayyukanta.

To ko wanene sabon Fira Ministan:

Abdiweli Mohamed Ali, ya kammala karatun digirinsa a makarantar Kennedy School of Government da ke Harvard, a Amurka.

Kuma tun daga lokacin ne yake koyarwa a jami'ar birnin New York, inda ya ke zaune tare da matarsa, wacce ita ma malamar jami'a ce.

Daga nan ne kuma makwafcinsa wanda ya zamo Fira Ministan Somalia bara, ya nada shi a matsayin mataimakinsa.

Hakan ya bashi damar sanin ayyukan da gwamnatin ke yi tun daga watan Nuwamban bara.

Ya kuma taka rawa wajen yunkurin sasanta kabilu a tsakiyar Somalia. Abin da ya bashi damar zuwa wani gari daban da birnin Mogadishu a matsayin jami'in gwamnati.

Abokinsa ya bayyana shi da cewa mutum ne mai rikon amana da kuma kwarin gwiwa.

Nadin na sa ya biyo bayan rushewar tsohuwar majalisar ministoci saboda karancin hada kai da Majalisar Dokoki.