An wanke Wilders bisa zargin sukar musulunci

Geert Wilders Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Geert Wilders ya bayyana farin ciki da hukuncin kotun

Wata kotu a Holand ta wanke dan siyasar nan Geert Wilders, wanda ya soki addinin musulunci, tana mai cewa yana da 'yancin fadar albarkacin bakinsa a bainar jama'a.

Mai shari'a Marcel van Oosten a birnin Amsterdam ya amince cewa kalaman na shugaban jam'iyyar Freedom Party sun shafi musulunci kai tsaye amma ba Musulmai ba.

Alkalin kotun ya ce "za a iya amincewa da kalaman idan ana tattaunawa ne a kan batutuwa a bainar jama'a"

Ana sa ran wadanda suka shigar da karar zasu sake kai batun gaban Kotun Tarayyar Turai ko kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Lauyansu Ties Prakken, ya shaida wa jaridar De Telegraaf ta Holand cewa ba su ji dadin hukuncin ba.

Sannan ya ce hukuncin ya tozarta batun kare hakkin marasa rinjaye.

'matukar farin ciki'

Alkalin ya ce duk da cewar kalaman na Mr Wilders suna da tsauri amma ba su kai ga haidar da wata kiyayya ba ga marasa rinjaye.

Magoya bayansa sun kece da tafi lokacin da aka sanar da hukuncin kotun.

Dan siyasar mai shekaru 47, ya shaidawa 'yan jarida a wajen kotun cewa ya yi "matukar farin ciki" da hukuncin".

"Ba wai kawai an wanke ni ba ne, wannan nasara ce ga ikon fadar albarkacin baki a kasar Netherlands".

An dai gudanar da shari'ar ce wadda aka fara a watan Janairun 2010, duk da cewa ofishin mai gabatar da kara na kasar ya nemi da kada a saurare ta.