Jam'iyyar Republican ta janye daga tattaunawa a Amurka

'Yan Republican sun fusata a Amurka
Image caption Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden.

'Yan jam'iyyar Republican sun janye daga wata tattaunawa da ake yi da nufin yiwa basussukan da ake bin Amurka linzami.

An yi tattaunawar ne a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasar Joe Biden.

Mista Biden ya ce kafin 'yan Republican din su janye an samu ci gaba mai ma'ana a tattaunawar.

Ya kuma kara da cewa yanzu dabara ta rage ga Shugaba Obama da kuma shugabannin jam'iyyun Republican da Democrat a majalisar dokoki, su gano hanyoyin warware bakin zaren.

Su dai 'yan jam'iyyar ta Republican sun fusata ne da yadda 'yan jam'iyyar Democrat suka nace sai an shigar da karin haraji a kan kamfanoni da mawadata wanda ya kai dala biliyan dari hudu a cikin kasafin kudin kasar.