Tattaunawa kan tattalin arzikin Girka

Shirin ceto tattalin arzikin Girka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Firayim Ministan Girka, George Papandreou

Shugabannin Tarayyar Turai sun shiga rana ta biyu ta taron da suke yi a Brussels inda suka shaidawa Girka cewa babu wani shirin ko-ta-kwana a batun ceto kasar daga tarkon basussukan da ta fada.

Ranar Alhamis ne dai shugabannin na Turai suka amince cewa wani sabon matakin tsuke bakin-aljihu ne akwai zai sa Tarayyar da Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, su baiwa kasar karin rance don ceto ta daga durkushewar tattalin arziki.

A makon gobe ne majalisar dokokin kasar ta Girka za ta kada kuri'a a kan matakan tsuke bakin-aljihun.

Shugabannin dai sun yi kira ga 'yan adawar kasar ta Girka su goyi bayan shirin.