Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Cutar hawan jini ga masu juna biyu

Image caption Yawancin mata masu juna biyun da ke mutuwa suna kasashen masu tasowa ne

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana mace-macen mata masu juna biyu da ce wa shi ne mutuwar macen da ke da ciki ko kuma wacce ta rasu a cikin kwana 42 bayan ta haihu.

Ko kuma ta wata hanyar da ke da alaka da goyon ciki, amma ba ta hanyar hadari ba ko kuma wata hanyar da ita da kanta ta janyo mutuwarta.

Acewar hukumar abubuwan da suka fi janyo mace-macen mata masu juna biyu ko yayin haihuwa a yankin Latin Amurka da Carrebean a sherarar 1997 zuwa 2002 su ne zubar da jini ba kakkautawa da hawan jini da kuma haihuwar da ta zo da gardama.

Haka kuma hukumar lafiyar ta bayyana cewa jijjiga wanda wani nau'in hawan jini ke jawowa ya dauki kashi goma sha biyu cikin dari na dalilan da ya janyo mutuwar mata masu juna biyu ko a yayin haihuwa a fadin duniya a shekarar 2005.

A kasashe masu tasowa a nan ne ake samun kashi 99 cikin dari na mace-macen mata masu juna biyu ko a yayin haihuwa dake faruwa a duniya.

Kuma wadannan kasashe su ne ke dauke da kashi 85 cikin dari na al'umar duniyar baki daya.

Kuma kasashe goma sha uku cikin goma sha hudun da matsalar ta fi kamari na nahiyar Afrika ta kudu da sahara, ciki kuma har da jamhuriyyar Nijar da Najeriya.

A shirin Haifi Ki Yaye da BBC Hausa na wannan makon, muna dauke da hira da Dr. Mairo Mandara wata kwarrariyar likitar mata dake Abuja ta yi karin bayani game da hawan jini da kuma abubuwan dake jefa mata cikin hadarin gamuwa da cutar a lokacin da suke da juna biyu.