Majalisar Wakilan Amurka ta yi watsi da kudiri kan Libya

Majalisar wakilan Amurka Hakkin mallakar hoto none
Image caption Majalisar wakilan Amurka

Majalisar Wakilan Amurka ta yi watsi da wani kudurin doka da ke neman amincewarta wajen shigar kasar cikin yakin da kungiyar NATO ta kaddamar kan Libya.

Majalisar ta kuma yi watsi da wani kudurin wanda ke son takaita yawan kudin da Amurkan ke kashewa a kan hare-haren da ake kaiwa a Libya.

'Yan Majalisar dai sun yi watsi da kudire-kudiren ne don nuna fushinsu ga Shugaba Barack Obama, bayan da ya shigar da kasar cikin yakin da ake yi a Libya ba tare da tuntubarsu ba.

Wannan dai shi ne karo na farko a cikin shekaru goma da Majalisar ta yi watsi da wani kudiri kan yakin da kasar ke son shiga.

Sai dai yin watsi da kudirin ba zai sauya yunkurin Amurkan na tsoma bakinta a cikin yakin da ake yi a Libya ba.