'Yan tawayen Libya na tattaunawar sirri

'Yan tawayen Libya na tattaunawar sirri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan tawayen Libya

'Yan tawaye a gabashin Libya sun ce a kullum suna tattaunawa da wadansu masu goyon bayansu cikin sirri a birnin Tarabulus.

A cewar 'yan tawayen, akwai daruruwan mutanen da suke tuntuba ta karkashin kasa a cikin birnin.

Sun kuma kara da cewa suna yunkurin tuntubar jami'an soji da 'yan sanda, wadanda a shirye suke su sauya sheka idan mulki ya kubuce daga hannun Kanar Gaddafi, wadanda kuma za su taimaka a hana asarar rayuka a birnin.

Yana da wahala a tabbatar da wannan ikirarin, amma wasu jagororin 'yan tawayen sun tabbatar da cewa akwai wani shiri mai kama da hakan.