Najeriya:'Yan Majalisa sun soki bukatar gwamnoni kan man fetur

Image caption Ginin da ke dauke da Majalisar Dokokin Najeriya

A Najeriya, wasu `yan majalisar Dokoki ta kasa sun yi suka kan kiran da gwamnonin kasar suka yi domin gwamnatin tarayya ta cire tallafin da take baiwa bangaren albarkatun man fetur.

Sun ce matakin wata hanya ce ta sake jefa al`ummar kasar a cikin kuncin rayuwa.

Su dai gwamnonin sun bukaci gwamnatin Tarayya ne ta janye tallafin domin a ba su kaso daga ciki, ta yadda za su samu damar biyan sabon tsarin albashi mafi karanci na naira dubu goma sha takwas.

Wani dan Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya shaidawa BBC cewa maimakon hakan, kamata ya yi gwamnati ta sake yin garambawul ga tsarin da ake bi na rabon arzikin kasar a tsakanin matakan gwamnati.