Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa matuka dangane da tabarbarewa tsaro a Yemen tun bayan da aka kashe mutane biyar a garin Aden jiya Juma'a.

Kwamitin Sulhun ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke rikici da juna a kasar su kai zuciya nesa, sannan ya bukaci a fara wani sabon yunkuri na magance rikicin ta hanyar siyasa.

Kwamitin ya kuma goyi bayan wani shirin samar da zaman lafiya na majalisar kasashen yankin Gulf; ya kuma goyi bayan wata ziyarar gani da ido wadda babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin bil Adama za ta kai kasar a mako mai zuwa.

Tun watan Janairu ne dai aka fara bore da nufin ganin bayan Shugaba Ali Abdullah Saleh wanda ya kwashe shekaru talatin da uku yana mulki a kasar.