Ra'ayi Riga: Tunawa da matan da mazajensu suka rasu

Matayen da aka kashe mazajensu a Iraq
Image caption Matayen da aka kashe mazajensu a Iraq

Jiya ce ranar farko da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe, domin tunawa da matan da mazajensu suka mutu.

Makasudin ware ranar shine: a fito da irin halin kaka-ni-kayin da irin wadannan mata ke shiga, da kuma irin wariyar da suke fuskanta, bayan rashin mazajen nasu.

A cikin watan Disamban bara ne, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kada kuri'ar amincewa da ranar, bayan wani kudiri da kasar Gabon ta gabatar.

Wani dan siyasar Birtaniya ne ya fara jagorantar wannan yunkuri, ganin cewa ya tashi maraya wajen mahaifiyarsa, bayan rasuwar mahaifinsa a Indiya.

An kiyasta cewa daga cikin irin wadannan mata miliyan 245 a duniya, miliyan 115 na fuskantar rashin adalci, da talauci da kuma azabtarwa.

Shirin ya gayyato baki da dama wadanda suka hada da:

Hajiya Aisha Muhtari .. Shugabar wata kungiyar kula da matan da mazajensu suka mutu suka bar su da ya'ya a Ghana.

Da Madame Mariama Musa... ta wata kungiyar dake kula da harkokin mata da yara a Jamhuriyar Nijar.

Da Hajiya Altine Abdullahi .... Shugabar kungiyar Zawarawa a Kano.

Da Mrs Christiana Yohanna, Daraktar harkokin mata a Ma'aikatar kula da mata ta jihar Pilato.

Da Ustaz Hussaini Zakariya ... wani Malamin Musulunci a Abuja

Da Reverand Sabon -yaro Adams ... Malamin addinin Kirista a Abuja.