An samu mace ta farko da laifi a yakin Rwanda

Pauline Nyiramasuhuko Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An sami Pauline da laifin shiryawa kai hare-haren kare dangi da yiwa mata fyade

Wata tsohuwar minista a gwamnatin Rwanda ta zamo mace ta farko da aka samu da laifi a binciken da ake yi kan kisan kiyashin da aka aikata a kasar.

Pauline Nyiramasuhuko ita ce minstar kula da iyali lokacin da aka aikata laifukan.

An shaidawa kotun hukunata masu laifi a yakin Rwanda cewa ta taimaka wajen shiryawa kai hare-haren kare dangi, da kuma na yi wa mata da kananan 'yan mata fyade.

Wakilin BBC ya ce, an fara shari'ar Pauline Niyirama-suhuko ne a watan Yunin 2001.

Yanzu shekaru goma bayan haka, alkalan kotun uku sun yanke hukuncin samunta da laifi.

Daga nan ne kuma alkalan kotun suka yanke mata hukuncin daurin rai-da-rai.

Kotun ta kuma yankewa danta ma hukuncin daurin rai-da-rai, bayanda aka same shi da laifin taimakawa wajen aiwatar da umarnin mahaifiyarta sa.