Zanga-zangar mako-mako a Syria

Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dubban jama'a ne suke fita kan tituna duk ranar Juma'a

Dubban jama'a sun sake shiga cikin zanga-zangar mako-mako da ake yi a sassa daban daban na kasar Syria, ta neman sauke shugaba Bashar al-Assad ya bar mulki.

Kamar dai yadda aka saba a kowace ranar juma'a a cikin kwanaki darin da suka gabata, wasu 'yan kasar ta Syria sun fita kan titina bayan da aka sauko daga massalacin Juma'a.

Dubban mutane ne suka yi maci a birane da garuruwa da dama, duk kuwa da irin matakan da mahukuntan suka dauka.

An bada rahoton an yi amfani da barkono mai sa hawaye da har ma da harbe-harbe a unguwar Midan dake tsakiyar birnin Damascus da kuma unguwar Al-Kisweh da ke bayan birnin.

'Juma'ar Karshe ta Amincewa da Mulki'

Kungiyoyin masu fafutuka sun ce akalla mutane tara aka kashe ciki harda jami'an tsaro.

A wasu wurare kuwa a kasar, masu zanga-zangar sun fita kan tituna ne, a abun da suka kira ''Juma'ar Karshe ta Amincewa da Mulki'' inda suke kiran da a hambarar da gwamnati.

A garin Salamieh da ke kusa da Homs, inda marassa rinjaye 'yan Ismaili suka fi yawa, mutanen da ba'a taba ganin yawansu ba, sun bijerwa matakin da jami'an tsaro suka dauka inda suka fita domin halartar wannan zanga-zanga.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jama'a na ci gaba da shiga Turkiyya domin tserewa rikicin

Ana ci gaba da samun barkewar zanga-zangar ne, yayin da dakarun kasar suke kara matsawa kusa da kan iyaka da kasar Turkiyya.

Amurka ta ce tana da matukar damuwa game da tashin hankalin da ake ciki kusa da wannan kan iyaka.

Kasashen Turai sun yi Allah wadai

Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin Syria da Turkiyya inda Turkiyyan tai kira ga gwamnatin Syria da ta kawo sauye-sauye.

Ko da yake gwamnati ta ce tana neman sulhu da yan adawa, to amma yanayin da ke kasa na tashe-tashen hankula ne kawai da kame-kamen Jama'a.

A gefe guda kuma kasashen Tarayyar Turai sun amince da wani daftari da ya yi Allah wadai da matakan da gwamnatin Syrian ke dauka wajen shawo kan masu zanga-zangar.

Abaya dai kasashen sun soki matakin na Syria, amma daga dukkan alamu hakan bai yi tasiri ba.

Kuma hakan ne yasa gwamnatin ta Syria ta yi barazanar daina hulda da kasashen Turai tana mai cewa za ta karkata akalarta zuwa kasashen Gabashi da kuma Asia domin huldar kasuwanci da kuma siyasa.

Sai dai Rasha da China sun ki amincewa su goyi bayan kudurin.