An yi wa Shugaba Chavez tiyata a asibiti

Shugaba Hugo Chavez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babu tabbas a kan tsananin ciwon

Ministan harkokin waje na Venezuela yace shugaba Hugo Chavez yana gwagwarmayar tsira da lafiyarsa bayan an yi masa tiyata a kasar Cuba.

Lokacin da yake magana a gidan Talebijin ministan harkokin wajen bai bayar da karin bayani ba akan halin da Mr Chavez yake ciki.

Wakiliayar BBC tace ba tare da bayar da cikkaken bayani ba, ministan harkokin wajen ya bayyana wa 'yan jarida na cikin kasar cewa kokarin samun lafiyar shugaba Chavez abu ne da ya shafi kowa.

Rahotanni dai sun ce Mr Chavez din yana farfadowa daga aikin da aka yi masa a kasar ta Cuba sakamakon kumbiri a kwatangwalonsa.

Sai dai akwai rade-radin da ake yi a Venezuela cewa halin da yake ciki ya wuce yadda ake zato.

Ba a san dai lokacin da Shugaba Chavez din zai dawo Venezuela ba.