Iran da makwabta za su yaki ta'addanci tare

Motar safa da aka kaiwa hari a Afghanistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aikin ba karami ba ne

Shugabannin Iran da Afghanistan da Pakistan sun fitar da wata sanarwa a tare inda suka ce sun amince su hada kai wajen yaki da ta'addanci.

Sun cimma wannan yarjejeniya ne a wani taro a birnin Tehran na Iran, wanda shugabanni daga Sudan da Tajikistan da Iraq suka halarta.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Iran ne ya bayar da wannan labari.

Kamfanin yace kasashen sun amince su yi aiki tare wajen yaki da tsaurin ra'ayi da kuma katsalandan