'Yan bindiga sun kai hari a wata mashaya a Borno

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Jihar Borno dake arewacin Najeriya, kawo yanzu hukumomi basu kammala tantance adadin mutane da suka rasu ba, sakamakon wani harin da aka kai a wata mashaya dake unguwar Dala Kabomti yankin Karamar Hukumar Birnin Maiduguri da kewaye.

Sai dai wasu majiyoyin sun ce mutanen da suka rasu sun haura ashirin.

Lamarin dai ya abku ne da maraicen jiya inda mutane da dama ke zaune a mashayar suna shakatawa lokacin da 'yan bindiga suka bude wuta kan mai- uwa- da- wabi, sannan daga baya suka jefa wani abu da ake kyautata zaton bam ne, wanda ya tarwatsa rumfuna da shaguna da dama a mashayar.

Rahotanni na nuna cewa, maharan dake kan babura, sun jefa bama bamai ne a cikin cunkoson mutanen dake mashayar.

Rundunar 'yan sandan Jihar Borno dai ta tabbatar da abkuwar lamarin, kuma ta dora alhakin harin akan Kungiyar Boko Haram, duk da dai cewa kawo yanzu babu wata kungiya da ta ce ita ke da alhakin kai harin.