'Yan tawaye sun ce suna jaddada iko a Libya

'Yan tawaye a Libya, sun ce suna cigaba da jaddada ikonsu a wasu wurare a kusa da Trablis babban birnin kasar.

'Yan tawayen dai sun kutsa ne daga inda suka fi karfi a tsaunukan Nafusa, kuma yanzu suna karawa da dakarun Gaddafi ne a wani wuri mai nisan kilomita 50 daga babban birnin kasar.

Amma wani wakilin BBC da ya ziyarci bakin dagar kusa da garin Bir al Ghanam, yace 'yan tawayen na fuskantar tirjiya daga dakarun Gaddafi.