Yau ake sa ran 'yan Majalisar Najeriya za su koma aiki

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya, a yau ne ake sa ran Majalisun Dokokin kasar za su koma bakin aiki bayan wani hutu da `yan Majalisun suka tafi na makwanni uku.

`Yan Majalisar dai kamar yadda suka bayyana sun tafi hutun ne domin su bai wa hukumomin Majalisar damar yi wa zauruka da ofisoshinsu wasu gyare-gyare.

Kuma sun tafi hutun ne ba tare da zaben wadanda za su rike wasu kananan mukamai a tsakaninsu ba.

Kazalika wasu abubuwa sun abku a Kasar ciki har da wadanda suka shafi harkar tsaro a lokacin hutun.

A bangare guda kuma, yayin da Majalisun Dokokin ke komowa bakin aiki, wani batu da Majalisar Dattawa za ta maida hankali akai shi ne tantance sabbin Ministoci da Shugaban Kasar ya mikawa Majalisar sunayensu a jiya.

Sai dai rashin fayyace Ma'aikatun da za'a tura Ministocin kafin a tatance su da kuma yadda wasu ke ganin Majalisar Dattawa ba ta yin aikin tantancewar yadda ya kamata na daga cikin batuwan da ke ci gaba da jan hankula Jama'a a Kasar.

Sai dai shugaban Majalisar Dattawan, Sanata David Mark ya ce, Majalisar za ta ci gaba da inganta yadda take yin aikin tatance Ministocin.