Wani Kwamiti na ci gaba da bincike kan rikicin Najeriya

Kwamitin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa domin binciko musabbabin rikicin da aka tafka a wasu sassa na Kasar bayan zaben shugaban kasa, da kuma wanda aka yi a Jihar Akwa Ibom kafin zabe, na ci gaba da sauraron ba'asi daga Kungiyoyi da sauran Jama'a a Jihar Kaduna.

Baya ga binciko dalilan tashin hankalin, an kuma bai wa Kwamitin alhakin gano irin asarar da aka yi ta rayuka da kuma dukiyoyi.

Kwamitin ya kuma fito da shawarwari ga Gwamnatin Kasar kan yadda za'a kaucewa sake samun afkuwar irin wadannan rikice- rikice a Kasar.

Rayuka da dukiyoyi da dama ne dai suka salwanta a rikice-rikicen da ake ganin ya janyo hannun agogo baya wajen kokarin hada kan 'yan Najeriya.