An saki wani dan adawa a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Hu Jia

An saki daya daga cikin fitattun masu adaw da gwamnatin China, Hu Jia, kuma yanzu haka yana tare da iyalinsa.

An saki Mista Hu ne bayan ya yi zaman kaso na tsawon shekaru uku da rabi a bisa tuhumar yiwa gwamnati zagon kasa.

An girka jami'an 'yan sanda masu dimbin yawa a kusa da gidan Mista Hu, wanda ga alamu yanzu ake yiwa daurin talala.

Kafin daure shi a shekarar 2008 dai Mista Hu mai fafutukar kare muhalli da masu dauke da cutar AIDS ko SIDA ne.