Alakar Sin da Birtaniya ta zarta ta tattalin arziki

A safiyar yau ne ake sa ran taron da ake tsakanin kasashen Birtaniya da Sin zai dangana da ofishin Prime Ministan Birtaniya dake Downing Street, inda David Cameron zai karbi bakuncin takwaransa na kasar Sin Wen Jiaobo tare da sauran ministocin Sin.

Kulla alakar cinikayya da ta al'adu na daga sahun gaba a ajandar ganawar, inda ake sa ran zasu cimma yarjejeniyar cinikayya ta fiye da pound biliyan daya.

Abin da suke son cimmawa shine kulla yarjejeniyar kasuwanci ta kimanin pound biliyan daya daga nan zuwa shekarard 2015.

Yarjejeniyar zata cike wani gibi a bangaren cinikayya da kasar Sin.

Masu fitar da kaya waje domin sayarwa na Birtaniya sun kara kimanin kashi ashirin cikin dari a adadin da suke fitarwa tun bayan da Prime Minista David Cameron ya ziyarci birnin Beijing a watan Nuwambar bara.

Gwamnatin Birtaniya dai na ganin wannan taron a matsayin wata dama ta gyara alakarsu da Sin a matsayin kawa ta samun ci gaba.

Ana sa ran cewa za'a cimma yarjejeniyar da zata baiwa Birtaniya damar fadada kasuwancinta a Beijing da Shanghai.

Sannan kuma akwai wani tsari na kulla alaka ta bangaren al'adu, kamar dai yanda sakataren harkokin da suka shafi al'adu a Birtaniya Jeremy Hunt ya ce.

Duk da dai cewa za'a tabo batun damuwar da ake da ita game da hakkokin bil adama a Sin, Birtaniya za ta ci gaba da nanata batun hakkin bil adama da ya kasance karkashin doka wadda zata baiwa Sin walwala da kuma daidaito na wani dogon zango.

Sannan kuma akwai damuwa game da irin martanin Sin akan abubuwan dake faruwa a yankin gabas ta tsakiya.

Sai dai ci gaban tattalin arziki da kuma ci gaban alakar diplomasiyya sun sha gaban komai.

Fatan dai shine lokaci na iya sauya halayyar gwamnatin Sin ta yanda take tafi da al'amuranta na cikin gida.