Yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Burtaniya da China

David Cameron da Wen Jiabao Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kasashen biyu na san habaka dangantakarsu ta fannin kasuwanci

Fira Ministan Burtaniya David Cameron ya ce an sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da ta haura dala biliyan 2 tsakanin Burtaniya da China.

Hakan dai ya faru ne lokacin ziyarar da Fira Ministan China Wen Jiabao ya kai Burtaniya.

Da suke magana a wurin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, shugabannin biyu sun ce suna fatan kasuwanci tsakanin kasashen biyu yakai dala biliyan 160 nan da shekara ta 2015.

Mr Cameron ya jinjinawa China kan yadda take baiwa 'yan kasuwar Burtaniya damar gudanar da harkokinsu a kasar.

Amma yace ci gaban tattalin arziki da na siyasa wajibi ne su tafi kafada-da-kafa da 'yancin bil'adama.

Mr Wen ya nemi da amaida hankali wajen hadin kai da bunkasa tattalin arziki, mai makon zargin juna.

Kayayyakin da Burtaniya ke fitarwa zuwa China sun karu da kashi 20 cikin dari, tun bayan ziyarar da Mr Cameron ya kai China.