ICC ta bada sammacin kama Gaddafi

Kanal Gaddafi
Image caption Gaddafi na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya

Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC, ta bada sammacin kame shugaban Libya Kanal Gaddafi da dansa da kuma wani na hannin damarsa.

Kotun na zarginsa ne da aikata laifukan yaki da bada umarnin kaddamar da hare-hare kan fararen hula bayan zanga-zangar nuna adawa da gwamnatinsa a watan Fabreru.

Kotun wacce ke birnin Hague, ta kuma bada sammacin kame wasu manyan na hannun damar Kanal Gaddafi - dansa Saif al-Islam da babban jami'in leken asirinsa Abdullah al-Sanussi.

Dubban mutane ne ake hasashen an kashe a rikicin.

Wani alakalin da ke jagorantar kotun ICC Sanji Monageng, ya ce a kwai shaidun da ke nuna cewa Kanal Gaddafi da dansa su ne da alhakin cin zarafi da kisan da aka yi wa fararen hular Libya.

Babban mai gabatar da kara na kotun Luis Moreno-Ocampo ne ya bukaci sammacin a watan Mayu, inda ya ce mutanen uku su ke da alhakin munanen hare-haren da aka kai kan fararen hula.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a kasar ta Libya

Mr Moreno-Ocampo ya ce kotun na da hujjojin cewa Kanal Gaddafi da kansa ya "bada umarnin kai hare-hare kan fararen hular kuma shi ke da alhakin kame 'yan adawa da cin zarafin abokan hamayyar siyasa.

A baya shugabannin Libya sun ce ba su amince da kotunba domin haka batun sammacin ba ya tayar musu da hankali.

A ranar Lahadi, mai magana da yawun gwamnatin Libya Moussa Ibrahim, ya ce kotun tana maida hankali ne kawai wajen hukunta shugabannin kasashen Afrika don haka "bata da wata kima".

Sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague, ya yi maraba da sammacin da , wanda ya ce "ya nuna yadda Kanal Gaddafi ya rasa duk wani goyon baya, kuma don haka wajibi ne ya bar karagar mulki".