Fargabar wata ambaliyar ruwa a Fagge dake Kano

A Jihar Kano dake arewacin Najeriya, mazauna yankin Fagge a birnin Kano na ci gaba da nuna fargabar sake fuskantar ambaliyar ruwa bayan wacce suka fuskanta a makon jiya, sakamakon abinda suka ce tafiyar hawainiya da aikin yashe magudanar ruwan da suka ratsa ta yankin ke yi.

Jama'ar sun ce a yanzu haka rashin daukan matakin yashe magudanar ruwan Kwarin Gogau cikin gaggawa, wacce ke daya daga manyan magudanar ruwan da ake amfani da su a birni Kano na barazana ga rayuwarsu da dukiyoyinsu.

A makon jiya hukumomi suka ce mutane sama da Ashirin ne suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata inda wasu kimanin dari uku suka rasa muhallansu sakamkon ambaliyar ruwa da ta biyo bayan wani ruwan sama mai yawa.

Sai dai hukumar kwashe shara ta Jihar ta ce ba ita ce ke da hakkin yashe magudanar ruwan ba, amma duk da haka za ta kai musu dauki.