An gano rumbun tara makamai a Libya

'Yan tawaye a Libiya sun kama wani katafaren wuri, inda aka boye makamai cikin ramuka, kusa da garin Zintan mai nisan kilomita dari da sittin, a kudu maso yammacin Tripoli, babban birnin kasar.

A 'yan kwanakin da suka wuce, jiragen sama na yakin NATO, sun kai hare-hare a wannan yanki.

Wani wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ce, a lokacin wani rami na ta ci da wuta, kuma ana iya jin karar fashewar bama bamai a karkashin kasa.