Yadda za a shawo kan matsalar rikicin Jos

Yadda za a shawo kan matsalar rikicin Jos Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a jihar ta Pilato

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa da wuya a samu zaman lafiya a tsakanin al`umomin jihar Plateau da ke arewacin Najeriya sai mahukunta sun rungumi dukkan kabilun dake jihar ba tare da nuna bambanci ba.

Adanm Higazi da ke sashen nazarin al`amuran da suka shafi nahiyar Afirka a jami`ar Cambridge ta Burtaniya, ya ce rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar yana da nasaba kai tsaye da addini da kuma kabilanci.

Kuma a ra`ayinsa akwai rawar da gwamnatin jihar za ta taka wajen shawo kan lamarin saboda ya gano cewa wasu `yan jihar na ganin cewa an mai da su saniyar ware.

Jihar Plateau dai ta sha fama da rigingimun addini da siyasa da kuma kabilanci wadanda suka yi sanadin asarar dimbin rayukan jama`a da dukiya.

"Samun zaman lafiya mai dorewa"

"Samun zaman lafiya mai dorewa a jihar Pilato akwai bukatar gwamnati duk da cewa yana da muhimmanci a bai wa kwararru guraban aiki, haka kuma yana da kyau a dinga rungumar dukkan al`umma da ke jihar wajen ba da aikin.

"Yin hakan a ganina zai taimaka, kuma jihar Pilaton ma za ta amfana daga hakan."

"Lallai sai an kamanta adalci zaman lafiya zai dawwama a jihar Pilato," a cewar Dr Husseini Abdu na kungiyar Action Aid wanda shi ma ya halarci taron.

Sai dai yayin da masana ke wannan hasashen mahukunata a jihar Pilaton na ganin cewa matsalar ta fi gaban kabilanci amma sun fara gano bakin zaren.

"muna iya kokarinmu wajen gano matsalar kuma tuni muka riga muka fara gano kan matsalar," a cewar Barrister Timothy Parlong mai bai wa gwamnan jihar Pilaton shawara a kan hanyoyin wanzar da zaman lafiya.

Jihar Pilaton dai za a iya cewa ta shiga bakin duniya sakamakon rigingimun da take fama da su wadanda ke sanadin asarar rayukan jama`a da dukiya.