Takaddama tsakanin direbobi da Kungiyarsu a Nijar

A Jamhuriyar Nijar wata takaddama ce ta kunno kai tsakanin wasu Direbobin tasi da Shugabannin Kungiyarsu, inda Direbobin ke zargin magabatan na su da yin sama da fadi da wasu kudade sama da Miliyan 177 na Saifa.

Kudin dai na daga cikin wani tallafi da Gwamnatin Kasar ta bai wa Kungiyoyin masu motocin sufuri dake gudanar da harkokinsu a cikin garuruwa.

Matakin kuma wani kokari ne na Gwamnati na hana masu motocin sufurin kara kudin mota, bayan da ta yi karin kudin mai a farkon wannan watan na yuni.

A yanzu haka dai rundunar Jandarmeri na can na yi wa Shugabannin Kungiyoyin 'yan tasin tambayoyi sakamakon karar da Direbobin suka shigar a gaban kotu