Ana wani gagarumin yajin aiki a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Birtaniya na fuskantar wani gagarumin yajin aikin da aka dade ba'a yi irinsa ba a cikin shekaru da dama.

Kungiyoyin kwadago sun bayyana cewa kimanin Ma'aikatan Gwamnati dubu dari bakwai da hamsin ne zasu taka rawa a yajin aikin, game da wasu tsare tsare akan kudaden Fenshon su.

Yajin aikin hadin gwuiwar dai ya hada da babbar Kungiyar kwadago ta Kasar da wasu Kungiyoyin Malaman makaranta uku a Birtaniya.

Wannan batun ma zai shafi dubban makarantu dake yankunan Ingila da Wales.

Tun a daren jiya ne yajin aikin ya fara tasiri.

A tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama, wasu Ma'aikatan Immigration sun ki zuwa wuraren aiyukansu.

Duk wanda ya isa Birtaniya a yau, akwai alamun zai dade a layin duba fasfo.

Gwamnatin Kasar ta yi zaton bai fi Kungiya daga cikin Kungiyoyin biyar din ne za su yi yajin aikin ba, sai gashi wannan ya sa duk wasu Ma'aikatu rufewa, tare da dage shari'u a kotu da duk wasu abuuwan kai kawo na ranar.

Babban matakin yajin aikin dai wanda zai damu iyaye matuka shine na yajin aikin Malaman makaranta.

Gwamnatin ta yi kiyasin cewa yajin aikin zai shafi akalla kashi biyu bisa uku na makarantun Ingila wanda yawansu ya haura dubu goma sha hudu.

Kungiyoyin Malaman makarantu dai na ganin hakan shi ne ya fi dacewa.

Kimanin Mutane Miliyan biyar ne ake cire musu kudaden fensho daga albashinsu, lamarin kuma da gwamnati ta ce ba mai dorewa ba ne, tare kuma da neman mutane su kara yawan shekarun gudunmawar da suke bayarwa a bangaren kwadago.

Wata Kungiya wadda itama ke taka rawa a wannan yajin aikin ta bayyana wannan matakin a matsayin cin zarafin dokokin kwadago, lamarin da wasu ke ganin cewa wannan ka iya sawa wadanda ke karkashin wannan tsarin su iya barin aikin ma baki daya.