Kungiyar tarayyar turai ta yaba wa kasar Girka

Masu zanga zanga a Athens Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga zanga a Athens

Tarayyar Turai ta yi marhabun da kuri'ar da aka kada a majalisar dokokin kasar Girka, ta amincewa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnatin kasar da ke janyo takaddama.

Ta ce, mahimmin mataki ne aka dauka, idan aka yi la'akari da mummunan halin da kasar ta shiga, na yiwuwar kasa biyan basusukan da ake binta.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce," mahimmin ci gaba ne aka samu, ta fuskar makomar kasar Girkan, da kuma game da dorewar kudin Euro gaba daya".

An yi artabu

Amma a kan titunan Athens, babban birnin kasar ta Girka, 'yan sanda sun yi ta artabu da daruruwan matasan da ke adawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin.

A gobe kuma ya kamata 'yan majalisar dokokin sun amince da wata doka, wadda ta fayyace yadda za a aiwatar da matakan rage yawan kudaden da gwamnatin ke kashewa.

Kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro, da kuma Asusun bada lamuni na IMF, sune suka bukaci gwamnatin Girkan ta tsuke bakin aljihunta, kamin su sakammata karin kudaden da za su taimaka mata, wajen biyan basussukan da suka yi mata kanta.

Wasu shaidu sun ce wasu masu zanga-zanga sun kutsa kai wani gini na daya ga daga cikin masu baiwa kasar tallafi Eurobank, inda suka yi yunkurin cinna masa wuta.

Sai dai 'yan sandan kwantar da tarzoma sun yi nasarar dakatar da su.