Hasashe kan tattalin arzikin Najeriya

Nigeria
Image caption Najeriya dai ta sha fama da matsalolin tattalin arziki

Bankin kasuwanci na Morgan Stanley ya yi hasashen tattalin arzikin Nijeriya zai habaka cikin gaggawa ta yadda za ta sha gaban Afrika ta Kudu nan da shekara ta 2025.

An yi wannan hasashe ne a daidai lokacin da ake ganin alamun samun bunkasar tattalin arziki a daukacin nahiyar ta Afrika.

Rahoton Bankin morgan Stanlin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar zai habaka da sama da kashi takwas bisa dari cikin shekaru biyu masu zuwa.

Kuma a cewar bankin, hakan za ta kasance saboda wasu abubuwa da dama. Mafi Muhimmanci daga ciki shi ne farashin mai.

Amma akwai wasu abubuwan da za su taimaka wajen bunkasar kasar, wadanda suka hada da karin albashin ma`aikata, wanda kuma zai yi sanadin karuwar kudi a aljufan masu karamin karfi.

Haka kuma shigar `yan kasuwa wajen samar da wutar lantarki za ta taimaka wajen kawo karshen matsalolin da kasar ke fuskanta da ke da nasaba da rashin wutar.

Babu tabbas kan Afrika ta Kudu

Bankin ya bayyana wasu hadura da ke tattare da rashin tabbas din siyasar kasar, sai dai ya nuna akwai haske a karshen lamarin.

Wannan rahoton dai ya zo ne a daidai lokacin da Jaridar Financial Times ta London ta ambato bankin Standard Chatered Bank cewar yana sa ran wata gagarumar habakar ciniki tsakanin Nahiyar Asiya da takwararta ta Afirka a cikin shekaru ashirin masu zuwa.

Sai dai babu tabbas game da makomar tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu.

Wasu tsauraran dokokin kwadago da barazanar mai da filaye da wuraren hakar ma`adinai mallakar gwamnati, da gwamnatin Jacob Zuma ke yi sun katse-hanzarin wasu game da harkokin kasuwanci a kasar.