An shirya taron yaki da halatta kudaden haram a Kaduna

A Najeriya wata kungiyar yan jarida mai yaki da halatta kudin haram ta shirya wani taro na kwanaki biyu a Kaduna.

Kungiyar ta shirya taron ne domin tattauna wa a kan wayar da kan yan jaridu a bisa hanyoyin dakilie halatta kudin haram,cin hanci da rashawa da kuma samar da kudade ga yan taadda.

Najeriya dai ta yi kaurin suna a idon duniya ta fuskar cin hanci da karbar rashawa,matsalar da hukumomin kasar suka ce suna kokarin dakatarwa,to amma a ganin wasu har yanzu akwai sauran rina a kaba.