Ala'adun aure a Najeriya

Ala'adun aure a Najeriya
Image caption Najeriya na da kabilu masu banbancin al'adu da dama

Rahotanni daga wasu sassan kudancin Najeriya na nuna cewa sha'awar aure na dusashewa a tsakanin samari.

Maza na dadewa fiye da yadda iyayensu maza suka yi ba tare da sun yi aure ba, yayin da mata gwagware suke ci gaba da damuwa ganin yadda lokacinsu ke kara kurewa.

Ko a tsakanin matasan ma'aurata ma dai al'amarin ba sauki.

Yadda su kan nuna halin ko-oho yi bukukuwa da dama wanda wani kan zaci ko tsarin aure na nufin koma da komai a gare su.

Sai dai lamarin ba haka yake ba a arewacin kasar - dokokin addinin Musulunci da kuma ra'ayin mazan-jiya na kare al'adun aure daga sake irin na Turawan Yamma.

A kudancin Najeriya akwai ire-iren aure guda uku - Na Musulunci, da na Kirista da kuma na gargajiya.

Rayuwa bayan bikin auren ce dai ke hana yawancin samari mayar da hankali wajen yin auren.

Wani matashi dan shekaru 20 a yankin kudu maso gabas ya ce bai isa ya yu tunanin aure a shekaru goman farko na fara aikinsa ba, ko da kuwa yana da takadar shaidar digiri, sai dai idan yana da iyaye masu hannu da shuni wadanda za su dauki nauyin bikin.

Hankalinsa zai kara ta shi idan aka ce budurwarsa ta kammala karatun digiri - domin zurfin karatun yarinya na sa ta kara tsada.

'Kashe Miji'

Sai dai idan mutum ya samu aiki a kamfanin mai ko na sadarwa, to bayan shekaru goma yana aiki, zai iya samun isassun kudaden da zai iya daukar nauyin duk irin rayuwar da matarsa ke son yi, da kuma samun cikakken iko a kanta.

A yankin kudu maso yamma yanayin ya sha bamban.

Ba sadaki ko kudin aure ne ke tayar da hankali ba, sai al'adu da ka'idoji.

Ga matashi a yankin, jin cewa mata na biyayya ba komai ba ne illa labarin kanzon kurege.

Abin da zai ci karo da shi shi ne cewa matarsa ta dauki tunanin Turawan Yammacin cewa mace daidai ta ke da mijinta kuma tana da damar bin tsarin rayuwar da ta ke so da kuma samun 'yanci a gida.

Ba mamaki ya yi ta korafi da kunkuni in ya ga dama - idan kuma da gaske yana son kawo karshen auren, to rabuwa ta kotu ita ce zabinsa.

Amma ganin yadda wannan hanya ke da tsada, masu wayo kan yi watsi da tsiwar matan na su - su ci gaba da al'amuransu.

Ana dai ganin cewa matan da kan nemi rabuwar aure ta hanyar kotu suna da imani sosai.

Wadansu kan nemi matsafa ne inda a kan yi amfani da hanyoyin gargajiya wajen kashe mazajen na su.

"Ya sabawa addini"

Daga baya kuma sai su shirya kasaitaccen bikin binne su, kuma da zarar an kammala zaman makoki, sai su ci gaba da sheke-ayarsu.

Har yanzu dai samari da dama kan je majami'u don yin aure ko da yake adadin masu zuwa ya ragu matuka.

A birnin kasuwanci na Legas, majami'un kan bari samari su auri 'yan matan da suka riga suka yiwa ciki.

Suna yin hakan ne kuma saboda sanin cewa iyaye da dama kan bukaci budurwar dansu ta haihu tukun kafin a daura aure.

A yanzu majami'u ba sa korar irin wadannan samari da 'yan matan; a maimakon haka, su kan hana amaryar ta sanya fararen kaya.

Bishop na majami'ar Anglican ta Amichi a jihar Anambra ta kudu maso gabas, Reverend Ephraim Ikeakor, ya yi watsi da al'adar wadancan majami'u.

Ya shaida wa shugabannin majami'arsa a makon da ya gabata cewa daura auren mace da namijin da suka riga suka samu ciki ya "sabawa addinin Kirista da kuma darikar Anglican", don haka ba zai amince da shi a majami'arsa ba.