An kara gano man petur a Kamaru

Taswirar Kamaru
Image caption Taswirar Kamaru

Gwamnatin kasar Kamaru ta bayyana cewa, an gano danyen man fetur a yankin arewacin kasar.

Hakan dai ya biyo wani bincike ne da kwararru suka gudanar, a wani yunkuri na binciko ma'adanan karkashin kasa a Kamarun.

Duk da cewa ba a kiyasta adadin man da aka gano ba, amma ana kyautata zaton cewa yana da yawan gaske, ganin cewa wurin da aka gano man yana makwabtaka da kasar Chadi, wadda tuni ta soma cin gajiyar man na petur.

Sai dai tuni wasu 'yan Kamaru din suka fara kukan cewa, ba wani alfanun da za su samu daga man petur din, ganin cewa a lokutan baya ma basu amfana da arzikin man petur din kasar ba.