Bangaren Mahamane Ousmane zai daukaka kara

Tutar Nijar
Image caption Tutar Nijar

A jamhuriyar Nijar, lauyan bangaren Alhaji Mahamane Ousmane na jam'iyyar CDS Rahama, ya ce, zai daukaka kara game da hukuncin da wata babbar kotun Yamai ta yanke akan wata takaddama a cikin jam'iyyar.

A wani taron manema labarai da ya kira a yau, Maitre Souley Oumarou ya ce kotun ta yi shari'ar ne ba tare da kasancewarsa, ko wani wakilin jam'iyar ta CDS Rahama ba.

Ya ce, hakan ya sabawa doka, saboda haka za su shigar da kara.

A ranar 29 ga watan Yuni kotun ta yi shari'ar sannan ta yanke hukunci a jiya.

Kotun ta ce, dakatarwar da bangaren shugaban jam'iyar Alhaji Mahamane Ousmane ya yi wa bangaren Alhaji Abdou Labo daga harkokin jam'iyar, ya sabawa ka'ida.