Cutar kwalara ta hallaka mutane 170 a Kamaru

Taswirar Kamaru
Image caption Taswirar Kamaru

An sake samun bullar annobar kwalara a yankin arewacin Kamaru.

Watanni biyun da suka wuce ne dai cutar ta soma bulla, inda kuma ta hallaka mutane kimanin mutane 170 daga cikin mutane fiye da dubu 2 da suka kamu da ita.

Hukumomin kiwon lafiya na Kamarun suna nuna fargaba dangane da sake bullar cutar, musamman ma a wannan lokaci na damina.

A sakamakon haka hukumomin lafiyar sun gargadi jama'a da su dauki matakan kariya da suka hada da tsaftace muhalli, da shan ruwa mai kyau, da dai sauransu.