Charles Okah zai iya fuskantar shari'a

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Nigeria, wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin cewa wasu mutane 4 za su iya fuskantar shari'a dangane da zargin ta'addanci.

Tun farko dai lauyoyin dake kare mutanen sun nemi kotu da ta yi watsi da karar. Ana Zargin mutanen da suka hada da Charles Okah da tada bam a ranar daya ga watan Octoban 2010 a Abuja, ranar da ake bukukuwan cikar shekaru hamsin da samun 'yancin kan Najeriyar.

Mutane dayawa ne suka hallaka, kuma wasu suka sami munanan raunuka a harin.