Kokarin tabbatar da tsaro a yammacin Afirka

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Shugabannin rundunonin 'yan sanda na kasashen yammacin Afirka na yin taro a Abuja, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaron da ke addabar yankin.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirkan ne, watau ECOWAS ko CEDEAO ta shirya taron.

ECOWAS din ta amince da gazawarta wajen magance kalubalen tsaro da yankin ke fama da shi.

Ta ce, taron zai baiwa jami'an 'yan sanda damar duba hanyoyin shawo kan matsalolin.

Yankin yammacin Afirkan dai na fuskantar matsaloli da dama, wadanda suka hada da karakainar makamai a tsakanin kasashen, da rashin tsaro a kan iyakokinsu, da kungiyoyin 'yan ta'adda, da dai sauransu.

Ita ma gwamnatin Najeriya ta na gudanar da wani taro na kwanaki biyu, don wayar da kan al`ummar kasar a kan harkokin tsaro.

Taron ya hada da masana da shugabannin addini da sarakunan gargajiya.

Najeriyar dai na fuskantar matsaloli da dama ta fuskar tsaro, ciki har da satar mutane don karbar kudin fansa, da kuma rikicin kungiyar Boko Haram da ya addabi wasu jihohin arewacin kasar.