Bincike kan satar jin sakonni a Birtaniya

David Cameron Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption David Cameron

Praministan Birtaniya, David Cameron, ya ba da goyon baya ga kiraye-kirayen da ake ta yi a kasar, cewa a yi wani bincike mai zaman kansa a kan abin kunyar saurare ko ganin sakonnin wayar wani.

Jaridar News of the World ce ake zargi da saurare da kuma da aikata hakan a kan dimbin mutane a kasar, ciki har da biyan kudi domin a nemo mata lambar wayar wata yarinya da ake zargin an kashe ta.

Mista David Cameron ya ce, za a soma binciken mai zaman kansa da zarar 'yan sanda sun kammala nasu bincike.

Jagoran 'yan adawan Birtaniyar, Ed Miliband, ya zarge shi da yin wani babban kuskure, yayin da ya nada tsohon editan jaridar News of the World, Andy Coulson, a matsayin Darektan watsa labaransa.

Tuni dai Mr Coulson yayi murabus daga mukamin.

Yanzu haka majalisar dokokin Birtaniyar na yin muhawara ta musamman a kan satar ji ko karanta sakonnin wayar wani.